Wata mata mai shekara 30 mai suna Zainabu Muhammad da ke zaune a kauyen Makwalla a Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna ta haifi ’yan hudu a gida cikin awa 20.
Matar wacce haihuwarta 12 ta haifi ’yan hudun ne a makon jiya bayan doguwar nakuda.
Malama Zainabu ta shaida wa Aminiya cewa ta gode wa Allah da Ya sauke ta lafiya duk da cewa ta wahala wajen haihuwar.
“Eh, ’ya’ya hudu na haifa, kuma a cikin dakin mijina na haife su domin ba mu da asibiti a wannan kauye. Babu kuma yadda za mu yi shi ne Allah Ya kawo min haihuwar cikin sauki a dakin mijina,” inji ta.
Da aka tambaye ta ko ta taba zuwa asibiti a duk haihuwarta sai ta ce, “A’a, ni ban taba zuwa ko’ina ba. Koda yake gaskiya na sha wuya a wannan karo domin ban yi tunanin zan rayu zuwa lokacin suna ba. Sai da aka rika karbo min maganin asibiti ina sha har Allah Ya sa aka yi suna kuma ko a yanzu ba na jin dadin jikina sosai, domin ko kwanan nan sai da na je na karbo maganina da na jariran.”
Tunda Zainabu ta fara haihuwa ta haifi ’yan biyu sau uku amma a wannan karo sai ta haifi ’yan hudu. Sai dai akwai wadansu daga cikin ’ya’yan nata da suka rasu a baya.
Malama Fatima wacce ita ce ta amshi haihuwar ta bayyana irin wahalar da uwar ta sha kafin ta haihu.
“Ni ce na karbi haihuwar yaran nan hudu amma fa gaskiya ta sha wahala sosai, kuma in ba don addu’o’i da rokon Allah da muka rika yi ba da ta rasa ranta saboda duk yaro guda da ta haifa sai da ta wahala. Sai ta kwashe sa’o’i biyar tana nakudar yaro daya kuma a haka ta haifi ’ya’yan hudu. Ga shi ba mu da hanya saboda wannan rafi da muke fama da shi babu wani taimako da muka samu na kai ta asibiti,” inji ta.
Ta kara da cewa: “Mu dai a kullum kiranmu ga gwamnati a taimaka a fito da mu gari domin har yanzu a karkashin kasa muke ba mu fito sarari ba,” inji ta.
A cewar mijinta mai suna Muhammadu Kabir Hassan, ta fara nakuda ne da misalin karfe 5:30 na yamma.
Ya ce matarsa ba ta taba zuwa asibiti ba domin a duba ta saboda babu asibiti a kauyen nasu da ke hayin kogi.
Malam Kabiru ya ce matan gida ne suka karbi haihuwar jariran hudu domin su a karkara mata ne ke amsar haihuwa. Amma yanzu biyu daga cikin jariran da ta haifa maza ne suka rage biyu sun rasu.
“Baki daya yanzu ’ya’yanmu takwas suka rag, domin haihuwarta 12 ne amma hudu sun rasu,”inji mahaifin yaran.
© hutudole
Post a Comment