Babbar kotun jihar Kano ta yanke hukunci ga wata mata mai suna Saude Yahya ‘yar asalin garin Utai a karamar hukumar Wudil, da ake zargi da hallaka jaririn da ta haifa.

 

Ana zargin Saude Yahya da samun juna biyu, daga wani bazawarin ta a lokacin da yake zuwa zance a soron gidan su.

 

Sai dai bayan da ta haife jaririn ne, sai ta makureshi har sai da ya rasa ransa sannan ta jefa shi acikin masai.

 

A zaman kotun na yau jumu’a Mai shari’a A.T Badamasi ya yanke wa Saude Yahya hukuncin daurin shekaru uku ko kuma biyan tarar naira dubu hamsin.

 

Cikakken labarin zai zo muku a shirin Inda Ranka na yau da karfe 9:30 na dare.

Freedomradio



© hutudole

Post a Comment

 
Top