A kokarin da gwamnatin Spaniya take yi na dakile yaduwar cutar Corona (Covid-19), ta hana mutane shiga kallon wasan da za a buga da kungiyoyin da suka fito daga kasashen da ake fama da cutar.

 

A wannan karon ma an yanke hukuncin buga wasan Valencia da AX Armani Exchange Milan ba tare da ba wa ‘yan kallo damar shiga ba.

 

An bayyana cewar an kuma a rage yawan alkalan wasa, jami’an lafiya, ‘yan wasa da jami’an kafafan yada labarai a wajen wasan.

 

A dakin wasanni na La Fonteta ne aka buga wasan na Valencia da AX Armani Exchange Milan a ranar Alhamis din nan.



© hutudole

Post a Comment

Emoticon
:) :)) ;(( :-) =)) ;( ;-( :d :-d @-) :p :o :>) (o) [-( :-? (p) :-s (m) 8-) :-t :-b b-( :-# =p~ $-) (b) (f) x-) (k) (h) (c) cheer
Click to see the code!
To insert emoticon you must added at least one space before the code.

 
Top