FITACCEN mawaƙi Nazifi Abdulsalam Yusuf, wanda aka fi da sunan Asnanic, ya bayyana mamaki kan yadda aka saka shi cikin jerin fitattun mutane 10 na Jihar Kano. Fim magazine na ruwaito.

A ranar Lahadi, 23 ga Fabrairu, 2020 wata jarida mai suna 'Guide Nigeria' ta wallafa wani jeri da ta kira fitattun mutane 10 na Jihar Kano inda ta lissafa har da Asnanic a matsayin mutum na shida a cikin su.

Jerin ya haɗa da su Aliko Dangote, Sanusi Lamiɗo Sanusi, Aminu Ɗantata, Aminu Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso, Amina Namadi Sambo da sauran su.

A hirar sa da mujallar Fim, mawaƙin ya bayyana farin ciki kan labarin.

Ya ce: "Gaskiya ni da na fara jin labarin tun farko na ɗauka shirme ne, sai na ga abin ya fara yawo a kafafen sada zumunta.

"Sai da hankali na ya dawo sai na yi wuf na nemi inda labarin ya fito. Ina dubawa, sai na ji wani iri, ma'ana na ke tambayar kai na yau suna na ne a tsakiyar su Ɗangote?

"Cike da mamaki da farin ciki, na ji daɗi sosai, don wannan cigaba ne a rayuwa."

Mawaƙin ya yi fatan alheri tare da jinjina ga Jihar Kano a kan irin cigaban da ta ke samu wajen ɗaga darajar addinin Musulunci.

Ya kuma yi godiya ga masoyan sa a kan ƙarfin gwiwar da su ke ba shi tare da mara masa baya, "saboda idan babu su to babu ni."

Asnanic ya ce, "Na gode ƙwarai da gaske."

Daga ƙarshe, ya yi wa masoyan sa albishir da cewa kwanan nan zai sako masu cigaban shahararriyar waƙar nan tasa mai taken 'Labari Na' wadda ya ke kan aikin ta yanzu.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top