Jagoran haramtacciyar kasar Biafra (IPOB) Mazi Nnamdi Kano zai jagoranci tattakin mutum milliyan daya a ranar 20 ga watan Yuni a Washington dake kasar Amurka, a kan zargin zalunci da cin zarafin Biafra da ake a sassa daban daban a Najeriya.
A cikin wata sanarwa da kungiyar IPOB ta fitar a ranar Juma’a ta hannun sakataren watsa labarai, Emma Powerful, ya bayyana cewa wannan gangami za su gudanar dashi ne domin ‘yantar da wadanda aka yiwa mulkin mallaka a Najeriya.
Ya bayyana tuni hukumomin Amurka da hukumomin tsaro suka bada Izini, inda ya bayyana da cewa za suyi hakane  domin su ja hankalin Duniya game da musgunawa da cin zarafin da ake yiwa Biafra a Najeriya.


© hutudole

Post a Comment

 
Top