Furodusan ya bayyana hakan ne a lokacin da su ke ganawa da wakilin mu, a kan shirye-shiryen da su ke yi domin yin wani kwarya-kwaryan fim da zai wayar da kan jama'a a kan cutar ta Corona Virus .
Furodusan ya fara da cewa "Shirin wayar da kai na cutar Corona Virus, hakki ne da ya rataya a kan gwamnati, ba a kan mu 'yan Kannywood ba, amma idan gwamnati ta bukaci mu yi wani shirin wasan kwaikwayo domin wayar da kai ai za mu yi, tun da ita za ta dauki nauyi ta kuma hada mu da likitoci kwararru ma su bincike a kan cutar su nuna ma na hanyoyin da za a bi domin magance ta, amma hakan nan ba za mu dauki jiki mu fara shirin wayar da kai a kan cutar da mu kan mu bamu san yadda zamu magance ta ba, ballan ta na mu wayar wa da jama'a kai". A cewar Mai Shadda.
Ya ci gaba da cewa, "Amma za mu yi matukar murna, har idan gwamnati ta jawo mu a jiki ta kuma bamu karfin gwiwar yin wannan shirin da zai iya zagayawa duk duniya ba wai iya Nijeriya kadai ba". Inji Mai Shadda.
Daga karshe, ya yi kira ga jama'a a kan a yi ta addu'a domin Allah ya kawo karshen wannan cutar ta Corona Virus ya kuma kare mu baki daya.northflix na wallafa.
©HausaLoaded
Post a Comment