Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa Najeriya na iya fuskantar karancin magunguna saboda dakatar da shigo da magunguna kasar da Indiya ta yi.

Makwanni biyu da suka wuce ne shugaban hukumar NAFDAC mai sa ido kan ingancin abinci da magunguna a kasar, Mojisola Adeyeye, ta ce Najeriya na iya fuskantar karancin kashi 70 cikin dari na magungunan da ake shigo da su daga wasu kasashen, a cewar jaridar.

Ta ce Indiya ta riga ta fara shiga halin ka-ka-ni-ka-yi saboda a China ta fi sayen kayan hada magungunan.

Wata sanarwa da gwamnatin Indiyar ta fitar jiya, wadda Shugaban hukumar cinikayya da kasuwanci da masana’antu Amit Yadav ya sa wa hannu, ta ce gwamnatin ta rage yawan magunguna masu muhimmanci da take fitar wa zuwa wasu kasashe saboda barkewar cutar coronavirus.

Gwamnatin ta ce ta dauki matakin ne don tabbatar da cewa tana da isassun maganin a kasarta, yayin da kwararru ke cewa kasar na iya fuskantar karancin magunguna idan annobar COVIS- 19 ta ce gaba.

BBC



© hutudole

Post a Comment

 
Top