Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da wa’adin kwanaki uku ga masu shaguna a kasuwar barci a jihar da su tattara su bar kasuwar a wata sanarwa da ta fitar.
Mazauna kasuwar sun tarar da sanarwar ne a safiyar Asabar a shagunansu inda sanarwar ke cewa gwamnatin ta ba kowa kwanaki uku kowa ya bar kasuwar.
Tun a kwanakin baya ake rade-radin cewa gwamnatin jihar za ta rushe kasuwar domin sauya mata fasali zuwa tsarin kasuwa ta zamani.
A takardar sanarwar, an bukaci masu rumfuna a kasuwar da su cire rumfunansu da kansu ko kuma su fuskanci fushin hukuma.
Yan kasuwar da dama sun koka dangane da wannan mataki inda wasu ke cewa an basu wa’adi a kurarren lokaci.
Malam Yahaya, wani mai shagon siyar da tufafi ne a kasuwar kuma ya shaida mana cewa akasari mazauna kasuwar ba su da wurin da za su je idan sun kwashe kayayyakinsu.
Shi ma Abdullahi Musa Sogiji wanda ke gudanar da sana’arsa a wannan kasuwa ya bayyana cewa kasuwar barci ta zama tamkar jami’a sakamakon irin jama’ar da take kyankyasarwa masu sana’a da za su zama masu dogaro da kansu.
Ya kuma yi kira da gwamnatin jihar Kaduna da ta sake tunani dangane da wannan mataki da ta dauka inda ya ce akwai jama’a da dama da ba su samun abin da za su ci sai sun je kasuwa sun bude shago sa’annan su samu na cefane.
Sai dai mun yi kokarin jin ta bakin Daraktan Hukumar Kula da Raya Birane ta Jihar Kaduna Ismail Dikko amma bamu same shi a waya ba.
© hutudole
Post a Comment