Cutar coronavirus ta kara fadaduwa zuwa mutum uku a legas, Kwamishinan lafiya na jihar, Farfesa Akin Abayomi, ya fada a ranar Alhamis da daddare.  Ya ce ban da mutumin Italiya da aka tabbatar ya kamu da cutar ta coronavirus (COVID-19), yanzu haka akwai mutane uku da ake zargin sun kamu da kwayar cutar a jihar Legas.
 kwamishinan lafiya Yace, yanzu haka akwai mutane uku da ake zargin sun kamu da kwayar cutar (COVID-19) a jihar Legas.
A wata sanarwa da ya wallafa ta a shafinsa na Tuwita: @ProfAkinAbayomi, ya ce: “A yanzu haka muna da wasu mutane uku da ake zargin sun kamu da cutar.  Daya daga Faransa, daya daga Ingila sai daya daga China. sannan ya bayyana an dauki samfuran su kuma ana tsammanin sakamakon. “


© hutudole

Post a Comment

 
Top