Tsohon dan wasan baya na Manchester United Rio Ferdinand yace odion ighalo ya karyata shi kan hasashen da yayi na cewa bai cancanci wasa a kungiyar ba

Ferdinand yana magana ne a BT Sport, ayayin da ighalo ya jefa kwallaye 2 a raga lokacin da suka yi nasarar wasan su da Derby county 3 : 0 a zagaye na biyar na gasar FA Cup.
Anyi tambayoyi da yawa, ayayin da Ole
Gunnar Solskjaer ya aro dan wasan gaba na Nigeria na tsawon watanni shida  a watan janairu.
Masu sharhi suna cewa ighalo wanda ya taba bugama Watford wasa na Premier League bai kai matsayin wasa a Manchester United ba.
Amma,Ighalo mai shekaru 30 a yanzu haka yana da kwallaye 3 a wasanni biyu kacal daya buga a garin.
Rio Ferdinand yace yawacin mutane da nima kaina muna tunani akan Ighalo, tayaya ya dace da irin wannan matsayin?
Ya kara da cewa imma ace kana da damar siyan dan wasa a farkon watan janairu,to ba shi ne ya cancanta ka siyo ba.
Saidai yace a yanzu  abin da Ighalo yayi ya kawo musu cigaba yakuma Kara ma garin maki.


© hutudole

Post a Comment

 
Top