Ma’aikatar shari’a ta jihar Kaduna ta tuhumi wani likita da ake zargin yana amfani da takaddun bogi, mutumin mai suna.

 

Saidu Ahmed Ya’u, an gabatar dashi a gaban wata kotun majistare saboda amfani da
satifiket din jabu da aikata ba daidai ba.
A wata sanarwa da ma’aikatar shari’ar, wacce babban lauyan gwamnatin jihar Kaduna, Aisha Dikko, ta sanya wa hannu, ta ce, ana ci gaba da tsare wanda ake zargi a Cibiyar Kula da gyaran hali dake Kaduna har zuwa 16 ga Maris.
Sanarwar ta kara da cewa Rahoton Bayanai na Farko (FIR) ya nuna cewa Saidu ya kasance yana aiki a matsayin likita sama da shekaru 11 a matsayin ma’aikacin sashin lafiya.
A cewar babbar lauyan gwamnatin, gwamna Nasir El Rufai ya umarci ma’aikatar kiwon lafiya da ta binciki Saidu, biyo bayan wata takaddar da ta shigar inda ta ce wanda ake tuhumar ya yi aiki da takaddun  karya. Ma’aikatar Lafiya ta kafa kwamiti mai mambobi hudu don gudanar da bincike da kuma tabbatar da takaddun shaida da cibiyoyin da Saidu ya ce ya halarta tare da tabbatar da rajistar sa ta shaidar Likitanci da Dental Council of Nigeria (MDCN).
A bayanan da Kwamitin ya bayyana yace Wanda ake tuhuma ya  manta takaddun Shaidar karatunsa Wanda ya gabatarwa hukumar lafiya ta daukan aiki,
A bayanan da Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya da Hukumar MDCN suka fitar, sun bayyana babu wata Shaida da suke da ita ga wanada ake tuhuma, kamar yanda Daily Trust ta ruwaito.
Alokacin da aka karanta masa tuhumar ya karyata
Daga karshe an nemi da aci gaba da tsare wanda ake tuhuma, Inda kotu ta dage zaman ta har zuwa 16 ga watan Maris.


© hutudole

Post a Comment

 
Top