Kasar Amurka ta saka ladar dala Miliyan 7, kwatankwacin Naira Biliyan 2.5 kenan ga duk wanda ya samar da labarin da zai kai ga kama shugaban kungiyar Boko Haram,Abubakar Shekau.

 

Sanarwa ta fitone daga shafin Twitter na hukumar dake kula da karrama mutane kan yin adalci ta kasar Amurka a jiya, Talata.

 

Shekau dai yana cikin mutane 10 na farko da kasar Amurka ke neman ruwa a jallo.

 

Kuma ya zama shugaban kungiyar ta Boko Haram tun bayan da aka kashe shugaban kungiyar na farko,Muhammad Yusuf.

 

Kungiyar tashi ta dauki alhakin kai hare-hare a manya-manyan gine-gine na gwanati, jami’an tsaro har dama majalisar dinkin Duniya.

 

Sannan ta kashe dubban mutane inda ta jefa sama da mutane miliyan 2 cikin halin gudun hijira.

 

 

 

 



© hutudole

Post a Comment

 
Top