Kungiyar dadtawan kabilar Igbo, dake Kudancin Najeriya Ohanaeze Ndigbo, tayi gargadin cewa Ndigbo bazata hade hannu ta bar Fulani makiyaya su ci gaba da musgunawa al’ummarsu ba, ta hanyar fyade da kashe mutanen yan kinsu.
Shugaban Kungiyar Ohanaeze, Cif Nnia Nwodo, a wata budaddiyar wasika da ya aike wa Sufeto-Janar na ‘yan sanda, mai taken,“ Hanyar fitina, ”a ranar Talata, ya ce Igbo a shirye suke dasu kare kansu daga duk wata fitina.
Nwodo, a wasikar sa ya bada labarin yadda yaran Fulani biyu suka fito da bindigogin AK-47 a fili cikin jama’ar Anambra inda kuma ya zargi Kwamishinan ‘yan sandan jihar da kin kama wadannan yaran,“ saboda sun fito daga wani yanki na kasar nan. ” a cewarsa.
Ya kuma tambayi Sufeto-janar na ‘yan sanda,“ Shin har yanzu ba a ba da izinin haramta mallakar bindigogi babisa doka ba ?
A rahoton da Jaridar Hutudole ta tattara Wannan bashine karan farko da kungiyar Igbo, Ohaneze Ndigbo suka aike da irin wannan wasikar ba, koda a shekarun baya Kungiyar ta aikewa shugaban kasa Muhammadu Buhari inda suka bayyana rashin jin dadinsu kan ayyukan Fulani Makiyayya a yankin kudu maso gabas, kamar yadda Jaridar Vanguard ta bada rahotan a wancan lokacin, inda kungiyar ta bayyanan bukatar hakan a ranar Alhamis, 29 ga watan Satumba a taron ranar Igbo na duniya a jihar Enugu.
© hutudole
Post a Comment