Hukumomi a Saudiyya sun kara daukar matakai a masallacin Ka’abah ciki har da rufe masallacin bayan Isha’i a kokarin kasar na dakile bazuwar cutar Coronavirus.

 

Wata sanarwa a Twitter da hukumomin da ke kula da Masallatan Haram a Makkah da Madinah suka fitar ta ce Masallatan za su kasance a rufe a cikin dare har sai zuwa sallar Asuba.

 

“Za a rufe Masallacin Ka’aba sa’a daya bayan sallar Isha’i, sannan za a bude shi sa’a daya kafin sallar Asuba a kullum,” in ji sanarwar.

 

Sauran matakan da hukumomin na Saudiyya suka dauka sun hada da rufe famfunan ruwan Zam-Zam da haramta cin abinci a cikin masallatan Makkah da Madina.

 

Sannan an rufe wurin Safa da Marwah sai yadda hali ya yi. Haka kuma an takaita wuraren da za a yi Sallah a cikin masallatan biyu.

 

Tun a ranar Laraba Saudiyya ta haramta wa ‘yan kasar yin Umrah saboda tsoron bazuwar cutar Coronavirus.

 

Tuni Saudiyya ta hana maniyyata zuwa Makkah da Madina, bayan haramta wa ‘yan kasashen da cutar ta yadu shiga kasar.

 

A ranar Litinin 2 ga watan Maris ne Saudiyyar ta tabbatar da bullar cutar ta Coronavirus a karon farko a kasar daga wani da ya fito daga Iran.

 

Hukumomin lafiya a kasar sun ce wanda ya shigo da cutar ya yi mu’amula da mutum sama da 50, ko da yake sun tabbatar da cewa gwajin da aka gudanar ya nuna ba wanda ke dauke da cutar.

 

Haramcin takaita ibada a masallatan dai zai ci gaba har sai lokacin da aka dage haramcin gudanar da Umrah a kasar.

 

Wasu da dama na nuna fargabar cewa tsoron cutar na iya janyowa a kasa samun damar yin Umrah a lokacin azumi har ma da aikin Hajji gaba daya a bana.



© hutudole

Post a Comment

 
Top