Wani jigo a jam’iyyar  (APC) a Kano, Alhaji Musa Danbirni, ya bayyana Namijin kokarin  gwamna Abdullahi Umar Ganduje na daukar ma’aikata 7,500 a duk kananan hukumomin jihar 44 a matsayin “babban matakin kawar da rashin aikin yi.

 

Ya yi wannan yabon ne a wani taron manema labarai a Kano ranar Jumma’a, inda ya ce kokarin da aka yi ya nuna yadda gwamna yake bawa bangaran ilimi muhimmancin inda ya Kara da cewa  daukar malamai 7,500 ya cancanci a yaba masa.
A karshe Danbirni ya yi kira da masu ruwa da tsaki da masu hannu da shuni da su tallafawa gwamnatin Ganduje a kokarin da take yi na ciyar da jihar gaba zuwa wani mataki na cigaba.


© hutudole

Post a Comment

 
Top