Tauraron dan kwallon Najeriya dake bugawa Manchester United wasa a matsayin aro, Odion Ighalo ya ciwa kungiyar tashi kwallaye 2 a karawar da suka yi a daren Alhamis na gasar daukar kofin FA da kungiyar Derby County.
IGHALOOOOOO#UndertheLights #DERMUN pic.twitter.com/TQTWgDwn9M
— The Emirates FA Cup (@EmiratesFACup) March 5, 2020
Shaw ne ya fara ciwa Man United kwallo gun kamin a je hutun rabin lokaci inda Ighalo ya kara kwallo ta 2. Bayan dawowa hutun rabin lokacine Ighalo ya kara cin kwallo ta 3 wanda a haka aka tashi wasan.
IGHALO at the double #UndertheLights #DERMUN pic.twitter.com/2N4jpDZv9a
— The Emirates FA Cup (@EmiratesFACup) March 5, 2020
Da wannan sakamako, Man United ta kai ga matakin wasan Quarter Finals inda zata hadu da Norwich.
Da kwallaye 2n da yaci, Ighalo ne ya karbi kyautar gwarzon dan wasan. Sankan ya kafa tarihin zama dan Najeriya na farko da ya ciwa Man United kwallaye 2.
Yanzu Ighalo na da kwallaye 3 kenan a shekarar 2020 wanda hakan ke nufin yafi Alexander Lacazette na Arsenal da Roberto Firmino na Liverpool yawan kwallaye a shekarar 2020.
Wasanni biyu kenan Ighalo ya bugawa Manchester United kuma ya ci kwallo a kowanne wasan.
© hutudole
Post a Comment