A ranar Alhamis ne majalisar dattijai ta amince da rancen dala biliyan 22.7 wanda Shugaba Buhari ya nema bayan wata muhawara mai zafi wacce majalisar tayi bayan rufe kofa da yan’ majalisun sukai wanda ya dauki tsawan mintuna 45 daga bisani kwamitin ya amince da kudirin abubuwa biyu lamunin gida dana waje, wanda Clifford Ordia ya ke Jagoranta.

 

Sanatocin sun hada kai kan batun tun farko game da takaddama wanda ya haifar da taron rufe kofar gaggawa, matakin da Sanata Gabriel Suswam ya ba da shawara.

 

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya ba da tabbacin cewa za a karkatar da rancen ne ga ayyukan da za su amfani rayuwar ‘yan Najeriya.

 

Ya kuma kalubalanci kwamitocin daban-daban na Majalisar Dattawa da su tabbatar da bin komai cikin kulawa.

 

Ya kuma bayyana cewa mafi yawan kudin, za’a samo su ne daga bankin ci gaban Musulunci, Bankin cigaban Afirka, Bankin Duniya da bankuna daga China, Japan da Jamus.

 

Abin dubawa anan shine bisa ga Ofishin Gudanar da Bashi (DMO), ya zama jimillar bashin waje ya kai kimanin dala biliyan 27.16, yayin da bashin cikin gida ya haura kimanin dala biliyan 56.72. kamar yadda jaridar The Sun Nigeria ta wallafa



© hutudole

Post a Comment

 
Top