‘Yan uwa da dangin wani yaro Usman Sanusi Abdullahi Maikano sun shiga jimami sakamakon tsintar gawar yaron dan kimanin shekara shida zuwa bakwai da aka tsinci gawar sa a unguwar su ta Farkon Idi dake cikin Birnin Sakkwato.

 

Lamarin wanda ya faru a jiya Alhamis 5/3/2020 inda wasu da ba a san ko su waye ba suka sace yaron,bkana suka sake kawo takardar neman kudin fansa, kafin cikar wa’adin kawo kudin fansar aka tsinci gawar yaron.

 

Mahaifin yaron, Alhaji Sanusi Abdullahi Maikano, ya bayyana kaduwar su akan lamarin.

 

“Abin ya bamu mamaki,nsun sace yaron, sun nemi mu ba su kudi kimanin naira dubu dari bakwai, kwatsam sai muka tsinci gawar yaron” inji shi.

 

Lamarin ya baiwa mutane mamaki, ganin cewa an saba idan an sace mutum zana iya kai kudin fansa, abbiya a sako shi,nsabanin na wannan yaron.

 

Wani abin mamaki shine irin kisan gillar da aka yiwa yaron.

 

“An yi mai kisan gilla, an sassare sassan jikin sa, tare da karairaye shi”, inji Hajiya Murja Gwaggon yaron.

 

“Ko su waye mun bar su da Allah, Allah ya shiga tsakanin mu da su”, inji Kakar yaron.

Rariya.



© hutudole

Post a Comment

 
Top