Gidauniyar Aliko Dangote (ADF) ta dauki alkawarin Naira miliyan 200 don tallafawa kokarin Gwamnatin Tarayya akan dakile yaduwar cutar Covid-19 (CoronaVirus) a kasar.
Ms Zouera Youssoufou, Babbar Darakta a Gidauniyar Aliko Dangote, a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata a Legas, ta ce bayar da gudummawar wani bangare ne na manufar gidauniyar.
 Youssoufou ta bayyana cewa, an ware kudi kimanin  miliyan N124 don tallafawa wuraren da za su taimaka wajen dakile sake bullar cutar da kayan aiki, musamman guraran shige da fuce na kasa,
A cewarta, burin gidauniyar dangote shine taimakawa gwamnati, wajan Samar da ingattaccen kiwon lafiya ga yan kasa.
Akwai kuma Miliyan 36 da aka ware wajan yin aikin binciken masu dauke da cutar sannan akwai kuma miliyan 48 itama da za’a y amfani da ita wajan horas da ma’aikatan da zasu yi wannan aiki da kuma sauran ayyukan gudanarwa.
Gidauniyar Dangote ta ware Naira Biliyan 1 dan tallafawa Nahiyar Africa yakar cutar ta Coronavirus.


© hutudole

Post a Comment

 
Top