Kamar yadda Kafar Hutudole ta rawaito akan batun Wata babbar kotun gwamnatin tarayya dake da zama a babban birnin tarayya,Abuja kan batun dakatar da shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole daga Mukaminsa.

 

Inda Maishari’a, Dalami Senchine ya bayyana haka, a ranar Laraba inda ya bukaci Oshiomhole ya sauka daga mukamin nasa har sai an kammala shari’ar dake neman a saukeshi gaba daya.

 

Tun bayan faruwar wannan hukunci, rahotanni suke bayyana Jam’iyar APC na shirin taron NEC don maye gurbin Oshiomhole.

 

Jaridar  PUNCH ta rawaito cewa wasu gwamnonin APC sun kara matsa kaimi don sanya wanda zai maye gurbin Oshiomhole a taron da gwamnonin jam’iyar za su zauna.

 

Wani jigo a jam’iyyar, wanda ya yi magana kan batun , ya ce, “Gwamnonin na shirin yin kiran taron Majalisar zartarwa ta kasa don duba lamarin.

 

Sai dai a labarin da ya iske kafar hutudole ya nuna cewa Shugaban jam’iyar APC Adam Oshiomhole ya daukaka Kara, Inda yake neman da kotu ta soke dakatar dashi da akai da kuma hanashi shiga harabar Sakateriya ta kasa, kamar yadda jaridar premium times ta wallafa, Sai dai kotun bata bayyana ranar da zata fara saurarar karar tasa ba.



© hutudole

Post a Comment

 
Top