Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi ta yi karin bayani game da hotunan da a baya tace zata saka tsirara-tsirara.

 

Nafisa a lokacin da ake tsaka da dambarwar fallasa hoton bidiyon abokiyar aikinta,Maryam Booth tsirara, ta bayyana cewa itama fa idan ta bushi iska za a iya ganin hotunanta daga ita sai rigar mama da dan kamfai.

 

Wannan rubutu da ta yi a shafin Twitter ya dauki hankula sosai ta yanda akaita maida martani kala da kala.

 

A yanzu Nafisar ta yi karin haske akan wadancan kalamai nata na farko.

 

Nafisa tace watau wasu suna tunanin zata biye musu ta saka hotunanta tsirara-tsirara, Busar Iskar data fada tana nufin yin abu bisa radin kanta bawai dan wasu suna so ba. Tace zaku jira ki gaji…

 



© hutudole

Post a Comment

 
Top