Cutar coronavirus mai saurin yaduwa, na barazana ga hanyoyin samun kudin shiga na Najeriya.
 a sakamakon haka , mai yiwuwa Gwamnatin Tarayya za ta sake duba kasafin kudinta na kimanin naira tiriliyan  N10.59 wanda Majalisar Wakilai ta kasa ta gabatar a ranar 5 ga Disamba kuma shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya  sanya hannu a kan doka a ranar 17 ga Disamba, 2019.
Ministar kudi, da kasafi da tsare-tsare na kasa, Zainab Ahmed ita ce ta bayyana hakan yayin da ta ke yiwa manema labarai karin haske ga wakilan majalisar a karshen taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC), wanda Shugaba Buhari ya jagoranta.
A cewarta, farashin mai na duniya ya ragu zuwa $ 52, a kasafin kudin da $ 57 kowace ganga.
Ministan, ta bayyana cewa arzikin man da kasar ke hakowa ya haura tsakanin ganga miliyan biyu da ganga miliyan 2.1 a kowace rana.
ta bayyana damuwar ta game da faduwar farashin mai, inda tace yanzu yana kasa da kasafin.
Sannan tasha al’washin yin nazari tare da duba kan yuwuwar sake duba kasafin.


© hutudole

Post a Comment

 
Top