Kakakin majalisar Jigawa ya bayyana a zauren majalisar cewa majalisar ta dakatar da dan majalisar dake wakiltar Gumel, Sani Isyaku a dalilin zargin yi wa tawagar gwamna dabanci.

 

Kakakin majalisar Idris Garba ya bayyana cewa Sani Isyaku ya ingiza matasa su yi wa gwamnan jihar Muhammadu Badaru dabanci.

 

Garba ya ce hakan karya dokar majalisar ne dama dokar kasa.

 

A dalilin haka majalisar ta dakatar da shi na tsawon sai wadda hali yayi. Wato ba ranar dawowa, sannan kuma ya umarce shi da ya maido da duk wani abu na majalisa dake hannun sa.

 

Bayan haka kuma ya kara da cewa majalisar ta kafa kwamiti domin bin diddigin abin da ya faru.

 

Sai dai kuma hakan bai yi wa dan majalisa Umar Danjani dadi ba duk da ba jam’iyyar su daya da Isyaku ba, wato shi yana jam’iyyar adawa ne.

 

Dan majalisa Danjani ya ce majalisar Jigawa ba ta yi wa Isyaku adalci ba dakatar da shi da tayi ba tare da ta gudanar da bincike ba.

 

Ya ce abinda ya fi dacewa shine a gudanar da bincike tukunna sannan a tabbatar da zargin kafin ma idan hukunci ne ma sai a zartas amma ba kawai majalisa ta yanke hukunci ba tare da ta bi diddigin abinda ya faru ba.

Premiumtimeshausa.



© hutudole

Post a Comment

 
Top