Gwamna Babagana Zulum ya bayyana cewa kiris ya rage da ya barke da kuka, a lokacin da ya ke raba kayan agajin jinkai da dimbin masu gudun hijira.

 

Zulum ya bayyana haka ne bayan aikin raba kayan abinci da sauran na masarufi ga masu gudun hijira da suka fito daga gidaje 19,000, a Gajiram, babbar hedikwatar Karamar Hukumar Nganzai ta Jihar Barno.

 

Gwamnan wanda shi da kan sa ne ya jagoranci dubagari da aikin sa-ido wajen raba kayan, ya ce ran sa ya baci matuka ganin irin halin kuncin rayuwar da Boko Haram suka jefa wadanda suka rasa muhallan su.

 

Sai ya ce, “shin har sai yaushe mutanen mu za su daina layin karbar abinci ne wai?

 

“Bai yiwuwa mu ci gaba da irin wannan rayuwar, wato rayuwar ci gaba da raba kayan abinci ga al’umma sun a shiga layi ana raba musu. Wannan abin takaici ne matuka.

 

“Ya zama wajibi ku bada hadin kai ga jami’an tsaro domin a kawo karshen wannan bala’i, ta yadda zaman lafiya zai dawo, kowa ya koma gidan su da kuma ci gaba da noma.

 

“Idan aka dubi irin kudin da ake kashewa wajen samar da abincin da ake rabawa din nan, sun isa a yi wasu muhimman ayyukan raya al’umma da su.

 

Daga nan sai ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da mazauna yankunan karkara su rika bai wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar ba su bayanan wasu bakin-idon da aka ga gilmawar su a yankunan su.

 

Kimanin matan aure 11,300 ne suka karfi atamfofi da naira 5000 kowace. Yayin da maza 7,800 suka karbi yadika da buhun shinkafa a na masara da lita uku ta man girki kowanen su.

 

Daga nan Zulum ya ziyarci Makarantar Firamare ta Mega da ke Gajiram a cikin Karamar Hukumar Nganzai, inda ya lura da yadda ake daukar sabbin dalibai masu shiga aji na daya.



© hutudole

Post a Comment

 
Top