Hukumar Hisbah ta Jihar Sakkwato ta kama wadansu mata biyu da ake zargin sun yi auren junansu (auren jinsi) suna zaune tare tsawon wata hudu. Hukumar na kuma zarginsu da shaye-shayen miyagun kwayoyi a Unguwar Obalande a Karamar Hukumar Sakkwato ta Kudu da ke Jihar Sakkwato.
Kwamandan Hukumar ta Jihar, Dokta Adamu Bello Kasarawa wanda ya jagoranci jami’ansa zuwa kamen, ya shaida wa Aminiya cewa “Wannan lamari da muke ji a wasu wurare ya zo mana nan, mace ta auri jinsinta, duk wanda ya ji haka zai yi mamaki yadda al’umma ke kara lalacewa. Matan sun yi alkawarin ba rabuwa a tsakaninsu ta hanyar sanya zobe da shan jinin juna don kara alakar.”
Ya ce: “Bincikenmu ya gano sun fara alaka da juna ne tun a Jihar Kaduna, kuma akwai wadanda suka sanya su cikin lamarin.”
Ita mijin mai suna Aina’u Ahmad Idris ’yar asalin Maiduguri ce mai shekara 23, ta ce ta kwashe sama da shekara biyu cikin wannan dabi’a.
“Alakata da wannan yarinya ta fara ce lokacin da zan zo Sakkwato daga Kaduna muka hadu da ita daga can ne muka fara hulda har na ja ra’ayinta mu auri junanmu tunda ba za mu iya yi wa junanmu ciki ba, ta amince na ba ta zobe ta yanki jinin jikinta na sha, na yanki nawa ta sha wanda hakan ke nuna mun kulla aure a tsakaninmu, mun fi wata biyu a tare kafin hukumar ta kama mu,” inji Aina’u.
Ta ce, ta yi da-na-sani sosai domin ta fahimci wannan abu da suke yi akwai kaskanci da saba wa Ubangiji a cikinsa. “Wata ce ta sanya ni cikin wannan harka a Kaduna mun yi shekara biyu tare kafin in dawo nan Sakkwato, a yau na tuba ga Allah zan koma makaranta kafin in samu miji in yi aure,” inji ta.
Matar mai suna Fatima Baba mai shekara 20 ta ki fadin asalinta, ta ce “Wannan abu da muka yi tsawon wata hudu ke nan sai daga baya ne na gane dokar kasa ba ta amince da yin haka ba, kuma addinin Musulunci bai yarda da haka ba domin ban dade da shiga addinin ba. Hakan ya sanya na kudiri aniyar barin wannan abu tun kafin Hukumar Hisba ta kama mu, ganin yadda akwai surkulle cikin lamarin. Wanda muke zaune a dakinsa duk sa’ar da za mu yi masha’a da junanmu sai ya shimfida mana wani jan kyalle, ya nuna mana ba ya samun kudi sai mun yi haka,” inji Fatima.
Ta ce in suna badala a gaban wanda ya ba su wurin zama sai ka ga ya kame jikinsa a gefe kamar mai sauraren wani abu, kuma ya kawo mata wadansu manya mata da manya motoci domin su tafi da ita wajensu ta samu kudi sosai abin da ya kara tayar mata da hankali har suka yi fada abin da ya kawo tonon asirinsu ke nan ta hanyar wata mata Zainab da ta sanar da Hukumar Hisbah abin da suke yi.
Abdullahi Isa wanda aka fi sani da 2pac shi ne wanda ya ajiye su a dakinsa ya ce taimakonsu ya yi domin ya hadu da su a gidan wasa na Solo ba su da wurin kwana, shi ne ya ba su wurin amma shi bai san suna wannan hali ba.
Ya yi kira ga malaman addini su tashi tsaye wajen karantarwa da ilimantarwa kan hadarin wadannan abubuwa na sabon Allah domin al’umma ta tsira daga fadawa cikin fitinnu.
Kan matakin da Hukumar Hisba za ta dauka kan mutanen da wadansu da ake zargi da irin wannan hali a Sakkwato, Dokta Adamu ya ce yanzu suna bincike don gano duk wata mafaka ta wadannan batagari don kama su da gurfanar da su gaban kotu.
© hutudole
Post a Comment