Majalisar dokokin jihar Kano a arewacin Najeriya ta kafa kwamiti domin bincike kan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II kan wasu korafe-karafe biyu da aka gabatar mata.

Majalisar ta kafa kwamitin ne ranar Laraba karkashin dan majalisa Zubairu Hamza Masu, wanda shi ne shugaban kwamitin sannan an bai wa kwamitin mako daya ya gabatar da rahotonsa.

A yayin zaman majalisar na ranar Larabar ne shugaban kwamitin ya shaida wa majalisa cewa ya karbi korafi biyu daga wata Kungiyar Bunkasa Ilimi da Al’ada ta Kano da kuma wani Muhammad Mukhtar mazaunin unguwar Ja’en a karamar hukumar Gwale a ranar Litinin.

Ya ce masu korafin sun yi zargin cewa sarkin Kano ya yi wasu abubuwa da suka saba mutuntaka da addini da al’adar mutanen Kano.

Zubairu Masu ya ce masu korafin sun gabatar da faya-fayen CD a matsayin shaida kan zargin da suka yi.



© hutudole

Post a Comment

 
Top