Iyalan Masarautar Saudiyya Ma Sun Kasance Suna Ziyartar Nijeriya Don Duba Lafiyarsu, Cewar Ministan Lafiya

 

Karamin Ministan Lafiya, Olurunnimbe Mamora, ya ce Nijeriya ta ci gajiyar kudin shigar yawon bude ido na kiwon lafiya kamar yadda PUNCH ta ruwaito.

Ministan wanda ya bayyana hakan a Abuja ranar Litinin, ya ce ‘yan wasu kasashe suna zuwa Nijeriya don neman magani a kwanakin baya.

Ya ce, “A cikin shekarun 50s zuwa 60s, Nijeriya ta amfana da yawon shakatawa na likitanci kamar yadda wasu daga cikin dangin sarautan kasar Saudiyya suka kasance suna zuwa Asibitin Koyarwa taJami’ar Ibadan don duba lafiyarsu.

“Wadansu mutane na balaguro zuwa kasashen waje don neman magani don kayan aiki da bamuda su akasar.

Muna da bukatar tabbatar da cewa muna da kayayyakin aiki a kasa wanda zai sa ‘yan kasarmu su dawo gida don neman magani.

Wannan ya hada da; kayayyakin rayuwa, ma’aikata, da kayan aiki.

“Aikinmu a matsayinmu na kasar shi ne sanya madaidaitan wuraren samar da magani don kula da lafiyar ‘yan ƙasa.

“Da zarar an samar da wadannan abubuwan, za a rage fita yawon shakatawa don ganin likita kuma zai sa asibitocinmu su zama masu kyau.”



© hutudole

Post a Comment

 
Top