Boko Haram sun kai hari a Dapchi, inda suka kashe wasu ’yan sanda 6. Haka Babban Sakataren Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA), Mohammed Goje ya bayyana.

 

Goje ya ce Boko Haram sun kai harin a ranar Laraba a Dapchi, wani kauye cikin Jihar Yobe.

 

Goje ya shaida wa manema labarai a Damaturu a ranar Alhamis cewa an dauko gawarwakin ‘yan sandan bayan kai harin wadanda ‘yan sandan mobal ne wadanda aka kashe din.

 

Sai dai kuma har zuwa lokacin da ya ke hira da manema labarai ba a tantance sauran gawarwakin farar hula biyu da aka kashe, ko su wane ne ba.

 

Shugaban na SEMA ya ce tsakanin ‘yan sanda, sojoji ko bilitante babu wanda ya iya shaida ko jami’an su ne ragowar gawarwakin biyu ba.

 

PREMIUM TIMES ta kuma tabbatar da cewa Boko Haram sun banka wa gidaje da dama wuta.

 

Dapchi can ne garin da Boko Haram suka sace daliban sakandare mata a cikin Fabrairu, 2018. Amma sun sake su daga bayan bayan sun kulla yarjejeniya da Gwamnatin Tarayya.

 

Sai guda daya kadai aka bari mai suna Leah Sharibu, wadda suka ki sakin ta, saboda sun nemi ta koma musulunci, ita kuma ta ki fita daga addinin Kiristanci.

 

Goje ya ce ya je Dapchi tare da wani jerin gwanon jami’an tsaro, tare kuma da Goni Bukar, wanda shi ne Kwamishinan Wasanni da Walwalar Matasa, wanda haifaffen Dapchi din ne.

 

“Don yanzu-yanzun nan ma muka dawo daga Dapchi din kamar yadda ku ke gani. Mun kwaso gawarwaki 8, wadanda 6 daga cikin su na jami’an ‘yan sanda ne. Biyu kuma wasu fararen hula ne da ba a kai ga tantance ko wasu wane ne ba.

 

Wakilin PREMIUM TIMES ya ci karo da jerin gwanon motocin da suka dauko gawarwakin bayan sun dawo daga Dapchi, inda ya yi ta bin su har cikin Asibitin Sani Abacha da ke Damaturu, inda kuma can ne aka ajiye gawarwakin takwas.

 

Goje ya ce ya bayar da umarnin a killace gawarwakin a dakin ajiye gawarwaki na cikin asibitin, domin iyalan kowace gawa su shaida kuma su tantance su, ta yadda za a rufe kowace kamar yadda ya dace a yi mata.

 

Shugaban na SEMA na Jihar Yobe ya ce Boko Haram sun kone sansanin sojoji da ke Dapchi da kuma wani sashe na ofishin ‘yan sandan garin. Sannan kuma sun banka wa wata motar sojoji wuta ita ma.

 

Sun kuma tsere da wata motar soja daya, kuma sun kone wata mota daya mallakar wani mutum mai suna Bukar.

 

Hakimin Dapchi, Yuroma Kamba, wanda ya gigita da wannan hari, ya yi kira ga gwamnati da a tashi a yi gagarimar addu’a a kan Boko Haram.

 

Wanda Ya Ki Gudu Shi Aka Kashe – Mazaunin Dapchi

 

Wani mazaunin Dapchi wanda ya tsere zuwa Damaturu, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan sandan mobal shida da aka kashe, sun rasa rayukan su ne saboda sun ki gudu, sun tsaya su yi bata-kashi da Boko Haram.

 

Ya ce amma ‘yan bijilante da sojoji duk arcewa suka yi a guje, yayin da suka ga kwamba din mahara gadan-gadan sun danno.

“Su ’yan sandan da aka kashe din ai tsayawa suka yi domin su tunkari maharan. Sojoji kuwa da ‘yan bijianti duk guduwa suka yi a lokacin da labarin maharan ya shigo cikin gari.

 

A wani labarin kuma an ruwaito cewa Boko Haram sun sha kashi a hannun sojoji a wani hari da suka yi yunkurin kaiwa a Damboa.

 

Wannan ya sa har Gwamna Babagana Zulum na Jihar Barno ya jinjina wa sojojin matuka.



© hutudole

Post a Comment

 
Top