Mai rukon mukamin shugabancin hukumar yaki da cin Hanci da rashawa takasa(EFCC), Ibrahim Magu ya karbi lambar girmamawa daga Ofishin  hukumar binciken Sirri, wacce aka fi sani da FBI dake kasar Amurka.
A lokacin da aka gabatar masa da lambar girmamawa a shalkwatar hukumar yaki da cin hanci takasa, EFCC dake Abuja,  Lauya mai wakilin hukumar FBI, Ahamdi Uche ya yaba da rawar da Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim magu ya taka yayin wani aikin hadin gwiwa da hukumar bincike ta FBI ta gudanar da aka yiwa lakabi da Operation Rewired.
 DAILY NIGERIAN ta  bayar da rahoton cewa, Operation Rewire hadin gwiwar yaki da laifuka ne da nufin magance matsalar Cin hanci.
A karshe hukumar  FBI ta yabawa shugabancin  Magu, da kuma hukumar bisa kokarin da take na yakar rashawa.


© hutudole

Post a Comment

 
Top