Bayan da wani ya saka hotunan hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad na da dana yanzu, lamarin ya dauki hankula inda har bashir din ya mayar da martani.
Abin ya farune a shafin Twitter inda mutumin ya saka hotunan tare da musu taken, #Sakamakon Chanji, Mungode Baba Buhari”
Sakamakon Chanji
Mun Gode Baba@BashirAhmaad pic.twitter.com/yjun2YFwAw— Local Sheikh (@sheikh_bash1) March 5, 2020
Bashir ya bayyana cewa an dauki hoto na farko ne a shekarar 2006 yayin da hoto na 2 aka daukeshi s shekarar 2020. Yace banbancin wancan lokaci da yanzu shine ilimin da ya samu. Yace duk da cewa an taba hotunan(watau an musu kwaskwarima)amma ya amince dasu. Saidai ya shawarci wanda ya saka hotunan da ya koma makaranta ya nemi ilimi dan ba zai so ganinshi a shekarar 2030 yana irin wannan abu ba.
Old pic taken in 2006 the other in 2020. Education brought me to where I am, I hope it will do same to you. Though both pictures were touched, but I am very grateful to Almighty Allah for the life and changes. Help yourself, I won’t love to see you in 2030 doing the same thing.
— Bashir Ahmad (@BashirAhmaad) March 5, 2020
© hutudole
Post a Comment