Hukumar da ke Sauraron Kararrakin Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta jihar Kano, ta gayyaci Mai Maratba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II da ya gurfanar a gabanta domin yi mata bayani kan badakalar filin da ya kai Naira biliyan 2 da miliyan 200.

 

Hukumar ta ce, tana bukatar Sarki Sanusi ya yi bayani kan saba wa sashe na 22 da 23 da kuma 26 na dokoki wajen sayar da kayayyaki mallakar Masarautar Kano.

 

Shugaban Hukumar Muhuyi Magaji Rimingado ya rubuta wasikar gayyatar Sarkin, inda ya bayyana cewar suna gudanar da bincike ne kan abin da ya shafi filayen da ake kira ‘Gandun Sarki’.

Daraktan hukumar, Usman Bello ya ce sun dauki matakin ne sakamakon korafin da wasu jama’a suka yi, ba tare da bayyana sunayensu ba.

 

Jami’in ya ce, bincikensu ya nuna cewar wani kamfanin da ake kira ‘Country Wide House Ltd’ ya taka rawa wajen halarta kudaden haramun daga kudaden da aka sayar da eka 20 na filin Masarautar Kano dake Darmanawa II.

 

Ya kara da cewar shi wannan fili an sayar da shi ne da umurnin Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II, yayin da aka sayar da wasu filayen da ke Hotoro da Bubbugaje ta hannun Shehu Muhammad Dankadai (Sarkin Shanu) da Sarki Abdullahi Ibrahim (Makaman Kano) da Mustapha Kawu Yahya (Dan Isan Lapai) da umurnin Sarkin.

RFIhausa



© hutudole

Post a Comment

 
Top