A ranar Talata, Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da tabbacin gwamnatinsa a shirye take ta aiwatar da shawarar kwamitin sulhu a kan rufe wasu hanyoyin iyakokin kasarnan.

Kwamitin ya hada da Najeriya, Benin da Nijar.
 A ganawara da Mista Bashir Mamman Ifo, shugaban bankin ECOWAS na zuba jari da ci gaba (EBID) da wanda zai gaje shi, Dakta George Nana Donkor, da ya yi a Abuja, Buhari ya yi bayanin cewa rufe iyakokin na wucin gadi ya baiwa Najeriya dumbin nasarori.
Shugaba Buhari ya bayyana dumbin Nasarori da hakan ya haifarwa Najeriya, Inda ya kara da cewa, tattalin Najeriya ya habaka, Najeriya ta dogara da kanta wajan Samar da abinci.
 “Mun hana shigo da muggan kwayoyi da kuma yaduwar kananan makamai wadanda ke barazana ga kasarmu,” in ji Shugaban.
Buhari ya gode wa Shugaban Bankin ECOWAS mai barin gado kan ci gaban da aka samu a lokacin mulkinsa na shekaru 8 sannan ya roki wanda zai gaje shi ya gina kan wadannan nasarorin.
A karshe Dr Donkor ya gode wa shugaban na Najeriya da jama’arsa saboda goyon bayan da suka bayar a lokacin da ya nemi mukamin.
 “Ba dan Najeriya ba, da ban yi Nasara ba,” in ji shi.


© hutudole

Post a Comment

 
Top