Wani mutum dan shekaru 47, Samuel Nweke, ya kashe kansa bayan Sun samu rashin jituwa da matar sa.
Lamarin ya faru ne a Awada, karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra.
Jaridar The Nation ta rawaito cewa matar Nweke ta bar gidansu a ranar 25 ga watan Fabrairu sakamakon rashin jituwa, wanda a sa kamakon hakan ne watakila ya haifar da kisan kan nasa.
Kakakin ‘yan sanda, Haruna Mohammed.
ya bayyana cewa Kwamishinan ‘yan sanda John Abang ya ba da umarnin gudanar da bincike , in ji Mohammed.
Kakakin ya ce, ‘yan sanda da ke binciken gawar Awada sun ziyarci inda lamarin ya faru, sannan suka dauki hotona sannan aka dauki hoton gawar mutumin bayan da likitocin suka tabbatar da cewa ya mutu.
Sannan likitoci sun tabbatar “Babu alamun tashin hankali a jikin wanda ya mutu.


© hutudole

Post a Comment

 
Top