Mutane 4 masu yiwa kasa hidma NYSC na 2019 da aka tura Bauchi ne suka rasa ransu a cewar Jami’in hulda da jama’a na shirin. Sun mutu ne a yayin aikin shekara daya, na wajubi na kasa, sannan mambobin kungiyar 14 ne za su maimaita hidamar aikin.

 

a cewar Jami’in hulda da jama’a na shirin Namadi Abubakar wanda ya bayyana haka a ranar Alhamis a yayin wucewa ga jerin gwano na shekara, Inda ya bayyana cewa mamatan sun mutu ne sakamakon kamuwa da cututtuka sannan daya ya mutun a Sa kamakon hatsarin mota.

 

Ya ce daga cikin mambobi guda 14 da suka yi kuskure, bakwai an kara aikinsu zuwa watanni hudu saboda laifuffuka daban-daban kuma sauran mambobi bakwai daga ciki an ba su sanarwar sake aikin nasu.

 

Abubakar ya lura cewa, takunkumin da aka sanya ga membobin kungiyar NYSC na kuskure shine domin karantar dasu da hana wasu aikata irin wannan aika-aikar.



© hutudole

Post a Comment

 
Top