Duk da cewa manajan gidan Radiyon Albarka dake Bauchi Waziri Hardawa ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa ya shirya wannan shiri ne domin wayar da kan mutanen jihar a matsayiun sa na dan jarida amma kuma ashe wai hakan da yayi ba daidai bane.

Hardawa ya bayyana cewa tattaunawa batun kawai akayi a filin shirin radiyon da bai sa ya ce komai ba amma kuma a karshe shine ya kwashi kashin.

Albarka Radiyo mallakin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar ne kuma tsohon shugaban gidan radiyon Tarayya, Ladan Salihu.

Hardawa ya kara da cewa ko a ranar da Ladan ya sallameshi a aiki ya bashi kyautar mota kuma har yanzu suna gaisawa.

” Ni na dauka a matsayina na kwararren dan jarida, ina aiki domin mutane da wayar musu da kai da kuma yada abubuwan dake faruwa da ya kamata su sani ne.”

Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES ta wallafa labarin yadda gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya dankara harkallar siyan motoci daga rantsar dashi sabon gwamnan jihar Bauchi ba tare da anbi yadda dokar kasa ta shimfida ba.

Kuma da yadda ya karkatar da kwangilar zuwa kamfaninsa. Duk da daga baya ya musanta cewa ba shi bane Balan da ya ke cikin jerin masu mallakin wannan kamfani da aka ba kwangilar.



© hutudole

Post a Comment

 
Top