Shahararren mawakin finafinan Hausa, Hamisu Sa’idu Yusuf wanda aka fi sani da Hamisu Breaker ya bayyana cewa batun da aka danganta shi da shi na cewa ya yaudari wata matar aure zuwa masana’antar finafinan Hausa ya dauki lamarin a matsayin kazafi kuma jarabta daga Allah. Kuma yana fatan Allah ya sa ya ci wannan jarabawar.

 

Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata wani mawaki mai suna Aliliyo Mai Waka ya zargi Hamisu Breaker da laifin yaudaro wata matar takwaransa mawaki Adam Fasaha zuwa cikin harkar fim.

 

An yi zargin cewa tun kafin jarumar mai suna Momee Gombe ta fito daga gidan mijinta mawaki Breaker yake hure mata kunne, wanda kuma bayan fitowar ta din ne aka soma ganin yana saka ta a bidiyon wakokinsa, wanda hakan ya sa aka sake tabbatar da zargin da ake yi masa.

 

Saidai a yayin da Breaker ya zanta da RARIYA, ya bayyana cewa “Wallahi zargin da ake yi masa babu madogara bare tushe. Kazafi ne kawai, don kawai an ga na soma samun daukaka shine ake so a bata min suna.

 

Breaker ya kara da cewa ko lokacin da aka saki Maryam din ya fi shekara bai yi ido hudu da ita ba.



© hutudole

Post a Comment

 
Top