Gwamnatin jihar Nasarawa ta bayyana kudirinta na dawo da dukkanin yara Almajirai da ke kasa da shekara 10, zuwa ainahin jihohinsu, kamar yadda Daily Nigeria ta ruwaito.

 

Kwamishina mai kula da harkokin mata ta jihar, Halima Jabiru ce ta ba da sanarwar yayin wani taron manema labarai bayan kammala taron majalisar zartarwa ta jihar a Lafia, babban birnin jihar.

 

Misis Halima ta lura cewa jihar tana da Almajirai kimanin dubu 63 wadanda suke yawo kan tituna.

 

A cewarta, sake haduwa da wadannan yaran zuwa ga iyayensu zai yi wa duniya kyau da al’umma baki daya.

 

Ku tuna cewa gwamna Abdullahi Sule ya ba da umarnin zartarwa wanda ya ayyana daurin shekaru 10 a gidan yari ga iyayen yaran da yaransu suke yin bara kan tituna a cikin jihar.

 

Gwamnan ya hana yin bara kan tituna a cikin jihar ya kuma ce gwamnati za ta inganta tsarin Tsangaya ta hanyar yin rajistar ɗalibanta a makarantun gwamnati.

 

“Wadanda suke bara a yanzu za a cire su a kan tituna kuma su yi rajista a makarantu don a kyautata rayuwarsu.

 

Mista Sule ya ce gwamnati ba za ta hukunta yaran da ke da hannu a rokon ba, amma za ta kakaba wa mutanen da suka tura su rokon.



© hutudole

Post a Comment

 
Top