Hukumomin Saudi Arabia yau juma’a sun bude Masallatan da suka fi kima a Duniyar Musulmi wato Ka’abah dake Makkah da kuma Masallachin Annabi Muhammad (SAW) dake Madinah domin cigaba da gudanar da ibadah bayan rufe su da akayi jiya domin tsaftace su daga kamuwa da cutar coronavirus.
Saudiya ta hana masu ziyarar Umrah daga kasashe 25 da kuma baki yan yawon bude ido ganin yadda cutar corona ke cigaba da yaduwa a kasashen duniya.
Gwamnatin Saudi tace ‘yan kasashen Yankin tekun Fasha da suka yi tafiye tafiye zuwa wasu kasashen da basa yankin dole sai sun zauna a kasashen su na kwanaki 14 kafin su ziyarci Makkah.
Ya zuwa yanzu hukumomin Saudiyar sun sanar da samun mutane 5 da suke dauke da cutar.
© hutudole
Post a Comment