Rundunar ‘yan sanda ta Ogun ta ce ta gano wata masana’anta da ake zargi da samar da jarirai a Imedu Olori da ke yankin Mowe a karamar hukumar Obafemi Owode na jihar.

Mai magana da yawun rundunar, Abimbola Oyeyemi (DSP) a cikin wata sanarwa da ya bayar a Abeokuta a ranar Alhamis, ya ce an gano gidan a ranar 28 ga Fabrairu.
Oyeyemi ya kara da cewa, ‘yan sanda, sunyi  wani abun a-zo-a-gani, yayinda sukai nasarar kubutar da wasu mata guda 12, wadanda shekarunsu tsakanin shekaru 20 zuwa 25 , inda  shida daga cikinsu na da ciki.
Ya kara da cewa wadanda ake zargi su uku sune: Florence Ogbonna, wanda ake zargin gidan mallakarsu ne.
Oyeyemi ya bayyana sun samu rahotanne daga wata da ta tsere daga gidan.
Ta kuma sanar da mu cewa mamallakin gidan Ogbonna shike kawo mazan da ke amfani dasu har su samu ciki.
A cewarta dazarar wata ta haihu, sai a dauke jaririn a tafi dashi wani waje da bawanda ya sani.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Kenneth Ebrimson, ya ba da umarnin a sauya wadanda ake zargin nan da nan zuwa satar mutane da satar kananan yara na Hukumar Binciken Laifukan’ yan sanda Sashen leken asiri don gudanar da bincike.


© hutudole

Post a Comment

 
Top