INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN

 

Nanin Kofar Nasarawa (Fulani Tafada) daya daga cikin manyan ‘ya’yan Sarkin Kano Halifa Muhammadu Sanusi ta rasu a daren yau.

 

Hakika wannan mutuwar ta girgiza ni matuka domin muna tare da baiwar Allahn nan a gidan makokin rashin da aka yi, dazun nan ta koma Gida ta rasu.

 

Allahu Akbar, an yi rashin hamshakiyar basarakiya mutuniyar kirki mai zumunci da hakuri, ba ta dauke ni sirika ba, kullum kamar ‘ya ta dauke ni.

 

Gimbiya ta k’i tafiya sai da ta zo tarota su ka yi hira, ashe sallamar bankwana suke yi, Allah Sarki.

 

Ta’aziyya ga dukka bani Dabo. Allah ya ji kan NANI ya gafarta mata, ya sa aljanna makoma.

 

Za a yi jana’iza da safe a Kofar Kudu gidan Mai Martaba Sarkin Kano.

Daga Sa’adatu Baba Ahmad



© hutudole

Post a Comment

 
Top