Kasar Italia ta sanar da rufe makarantu da jami’oin kasar baki daya daga yau laraba har zuwa ranar 15 ga wata saboda mutuwar mutane 107 da suka kamu da cutar coronavirus.

 

Wannan mataki shine mafi tsauri da wata kasar Turai ta dauka sakamakon barkewar cutar bayan taron kasashen G7 masu karfin tattalin arzikin duniya.

 

Hukumomin Italia sun ce yau larabar mutane 28 suka mutu, wanda shine adadi mafi yawa tun bayan barkewar wadda aka tabbatar ta kama mutane sama da 3,000.

Rahotanni sun ce hukumomin kasar na cigaba da nazari wajen daukar matakin gudanar da gasar kwallon kafar Serie A ba tare da ‘yan kallo ba na wata guda domin dakile yaduwar cutar.



© hutudole

Post a Comment

 
Top