Suna: DAN YAU
Tsara labari: Dan Azumi Baba.
Kamfani: A.U.K Entertainment Tare Da AU MAFARAS NIG LTD.
Shiryawa: Auwalu Uba Kwakwatawa.
Bada Umarni: Nura Sharif.
Sharhi: Musa Ishak Muhammad.
Jarumai: Ado Isa Gwanja, Shehu Hassan Kano, Sulaiman Bosho, Isiyaku Abubakar Jalingo, Hajara Usman, Malam Inuwa, Teema Yola, Hajiya Hadiza, Baba Duduwa, Baba Labaran da sauransu.
Labarin fim din DAN YAU labari ne a kan wani matashi mara jin magana, mai suna Hudu (Ado Isa Gwanja) wanda ya addabi kowa a wannan gari, rashin jinsa bai tsaya ga yaro ko babba ba. Hasali ma iyayensa ma wato NaLami (Shehu Hassan Kano) da kuma Lantana (Hajiya Hadiza) bai kyale su ba, domin kuwa kullum cikin bata musu rai yake saboda goyon bayan da yake samu daga gurun kakarsa wato Gwaggo (Hajara Usman).
A farkon fim din an hasko Audi (Isiyaku Abubakar Jalingo) yana tafiya a kan keke yana dan yin wake-wake, yazo ya wuce wasu yara suna wasan kwallon kafa. Yana kan wannan keken ne, sai suka hadu da Gwaggo a kan hanya inda ya yi kanta da keken yana shirin buge ta, aikuwa a nan ne ta tsaya tana ta kwashe masa albarka da kuma yi masa mugayen addu‘o’i. Bayan sun gama hayaniyarsu da Audi ta yi gaba to a nan suka hadu da Malam Liman (Malam Inuwa) inda yake mata fada a kan cewa bai kamata ta ringa la’antar ‘ya‘yan mutane ba tana tsine musu, domin kuwa idan tsinuwarta ta kama yaron to ba iya kan shi za ta tsaya ba domin za ta iya shafar jama’ar garin gaba daya, a nan dai
shi ma ta fada masa bakaken maganganu ta yi tafiyarta.
Daga nan gurun gwaggo ba ta tsaya a ko’ina ba sai gidan danta wato NaLami, wanda kuma shi ne mahaifi ga Hudu wanda aka fi sani da “Dan Yau”,tana shiga gidan ne ta iske Nalami yana dukan Hudu a kan sai ya fita ya tafi gurun wani aikin kamar yadda sauran maza suke yi, shigowarta ke da wuya, ai kuwa ta kama fada a kan cewa ita fa a daina dukar mata jika, ta rufe Nalami da fada kuma tana musu gargadin kar su kara dukan shi a cikin wannan gida.
A nashi bangaren, shi Hudu wato Dan Yau yayi shuhura wajen cin mutuncin mutane da wulakanta su da yi musu rashin mutunci da wulakanci kala-kala, abun nasa bai bar kan mata ko maza ba, ko yara ko manya, duk wanda rashin mutuncin ya biyo ta kansa to zai yi masa ne kawai. A sanadin haka ya karya wasu, ya jikkata wasu, ya kuma janyo wa wasu kuma asarori masu yawa. Haka ya yi ta rashin mutunci a cikin garin nan ba a tanka masa saboda goyon bayan kakarsa da yake samu a kowanne lokaci. Iyayensa kullum suna iya kokarinsu wajen saita tarbiyarsa amma hakansu ya kasa cimma ruwa saboda dakile duk wani yunkurunsu da gwaggon ta keyi.
Dan Yau bai fara samun matsin lamba ba har sai da rashin mutuncinsa ya dira a kan Inna (Baba Duduwa) wacca mahaifiya ce ga mai gari wato (Sulaiman Bosho) lokacin da ya fasa mata goshi da dutse. A sakamakon haka ne mai gari yasa aka fara farautar Hudu ba dare ba rana, amma ba a samu nasarar kama shi ba wanda hakan ya tilasta kamo mahaifinsa domin a yi masa hukuncin da za a yi masa. A haka dai mai gari yasa a ka ringa yi wa Nalami wulakanci kala-kala da hukunce-hukunce da aka yiniyar yi wa Hudu.
A karshe dai Gwaggo ta yi yunkurin guduwa da Hudu daga wannan gari saboda neman shi da ake yi ruwa-a-jallo wanda mai gari da sauran jama’a suke yi. Bayan mai gari ya samu rohoton cewa ga Gwaggo chan tana shirin guduwa da Hudu da abokinsa Audi, nan take ya sa a ka bi su kuma a ka yi nasarar kama su da jami’an tsaro bayan sun shigo mota suna yunkurin guduwa. A nan ne jami’an tsaro suka kamo su suka dawo da su kuma a ka gurfanar da su a fadar mai gari,wanda a karshe ya yi wa jami’an tsaro umarni a kan su tafi da su domin yi musu hukunci daidai da abinda suka aikata.
ABUBUWAN YABAWA
1. Labarin ya tsaru kuma ya yi nasarar rike mai kallo tun daga farko har karshen fim din.
2. Yanayin daukar hoton ya yi kyau kuma an samu sauti mai kyau.
3. Jaruman sun yi kokari a kowacce fitowa a cikin fim din.
4. Wurin da aka dauki fim din ya dace da labarin.
KURAKURAI
1. Marubucin ya so ya nuna cewa yawan tsinewa ‘ya‘yan mutane da gwaggo take yi da kuma aibata su, shi ne abinda ya afkawa jikanta Hudu, to ya kamata a ce ya nuna rayuwar Hudu sanda yana karami, sannan sai ya taso da dabi’un marasa kyau, amma sai gashi sai bayan ya girma ya zama saurayi sannan ake nunawa mai kallo gwaggo tana tsinewa ‘ya‘yan mutane da kuma aibata su.
2. Kayan da Hudu yake sanyawa shi da abokinsa Audi sam ba su yi kama da shigar kauyawa ba, kuma gashi ba a bayyana cewa ‘ya‘yan masu hali bane, kuma ba a nuna suna da wata sana’a ba balle mai kallo ya yi zaton cewa siyowa suke yi da kudinsu su saka.
3. Bayyana Rabi a matsayin Aljana kuskure ne,domin tun a farkon fim din an nuna mutum ce domin kuwa an hasko ta lokacin da mahaifinta yake fada mata cewa Hudu ya karya shi. To daman mutum yana iya komawa aljani wata rana kamar yadda aka nuna a cikin fim din?
4. Wakar da Hudu yazo yana yi a fada bayan an kamo su wadda har aka nuna mai gari yana tikar rawa kwatakwata ba ta dace da gurbin da aka saka ta ba, domin su masu laifi ne ta ya ya har za a basu damar yin waka kuma a fadar? Sannan bayyana mai gari yana tikar rawa a cikin fada a gaban jama’a bai dace da tsarin shugabanci na masarautun Hausawa ba.
5. Ya kamata ace an nuna wani hukunci mai tsauri da za a yi wa Hudu duba da irin ta’asarda ya aikata,wanda hukuncin zai saka shi yin nadamar abubuwan da ya aikata.
KARKAREWA
Fim din “Dan Yau” ya yi kokarin nuna illar aibatawa da kuma tsinewa ‘ya‘yan mutane. Saboda halin gwaggo shi ne ya janyo wa jikanta samun wannan dabi’u munana, wanda hakan ya addabi kowa da kowa a wannan gari, sannan ya nuna illar nunawa ‘ya‘ya ko jikoki gata wanda ya wuce ka’ida, domin hakan yana janyo nadama a karshe. A karshe dai, fim din ya samu aiki mai kyau kuma an yi kokari sosai a cikin aikinsa, duk da matsaloli da aka samu a wasu wurare.
©HausaLoaded
Post a Comment