Kwanakin baya na yi ta samun korafi daga bakin mata suna kawo kokensu akan miskilan maza. Da yawa na takaicin halayyar irin wadannan mazaje saboda dabi'arsu ta nuna halin ko in kula.

Duk da ansan cewa dabi'ar mata ce yawan magana, babban rauninsu a rayuwa kuma shine "so", sabili da emotional side dinsu. Inda a maza ba haka abin ya ke ba, kamar yadda na karanta a cikin littafin "Men are from Mars, Women from Venus", inda na gane bambance-bambance da ke tsakanin mace da namiji.

Wasu na ganin cewa miskilanci ra'ayi ne, wani bangaren kuma na ganin halitta ce. Akwai taken da Bahaushe ya yi ma miskili cewa, "kafi mahaukaci ban haushi".

Ana kallon miskilin mutum a kan cewa mutum ne shi mai girman kai, da jiji da kai, mutum mai wulakanci wanda sam ba haka bane ba. Yanayin halittar shi ce haka ta rashin son magana da kuma shiga abinda bai shafe su ba. 

Alal hakika ba'a fahimci ya rayuwar miskili ta ke ba, shi yasa da yawa daga cikin mutane ke gudunsu, ana masu kallon wadanda basu da dadin sha'ani. Wasu ma a kan yi tunanin ko basu da cikakkiyar lafiya ne, ko kuma matsalar jinnu ke damunsu, kowa da irin tunaninshi akan miskilin mutum.

A wani bincike da aka gudanar a jami'ar Waterloo da ke Ontario a kasar Canada, inda aka ware kamanin dalibai 480 dan gudanar da bincike a kansu. Inda aka ware dalibai 290 wadanda ba miskilai ba, sannan aka samu 190 wadanda sune miskilai, kuma sune wadanda suka fi kokari da wayau a cikin makarantar.

Akwai tambayar da na samu daga wajen ƙawata a kan ta ya za ta bullowa miskilin saurayinta, abin na matukar damunta.

Na tausashe ta, tare da ba ta wasu yan dabaru. Matsalar da ake samu shine da yawan mata saboda yanayin dabi'ar mu ba mu san yadda zamu tafiyar da miskilin namiji ba, wanda sai mu ga kamar rayuwar aure ba za ta yiwu a tsakaninmu ba.

Zan kawo mana dalilai da za su gamsar da mai karatu dalilan da kan sa a so miskilin namiji har ma a yi tunanin ya fi sauran maza dadin zama bisa ga binciken da Dakta Barbara Markway masaniya a kan halayyar dan Adam ta yi a shekarar 2011. 

1. Suna da kokarin sauraren mutum

Da yawan miskilai idan aka zo batun su saurari mutum suna cikin sahun farko na mutane masu saurare, maimakon kuyi ta musayar kalamai da su, sai su kasance suna sauraron mi ki ke cewa, ba wai sauraro irin ya shiga kunnen dama ya fita ta hagu ba, a'a za su saurari duk bayaninki bil hakki da gaskiya sannan su samu matsugunin da za su ajiye maganar.

To a nan an sha bamban, mafi yawan mata basu son wannan dabi'ar. Mata sun fi son suna magana ana maida yanda aka yi, to daga ta ga an yi shiru sai ta harzuka ta ga kamar da kanta kawai take magana. Daga nan matsala za ta fara kunno kai saboda an samu sabanin fahimtar juna.

Mata ku fahimci wani abu guda dangane da miskilin namiji a duk lokacin da ki ka gama bayaninki yana daukar duk wata kalma da ta fito daga bakinki mai muhimmanci.

2. Samun isashshen lokacin magana

Kamar yadda na ambata a farko, za ki samu isashshen lokacin da za ki duk wata magana da za ki yi ba tare da anyi interrupting dinki ba. Kina da yancin ki fadi duk abinda ki ke so, babu wata gardama unlike wasu mazan da ba za su bari ma ki fadi jimla daya ba za su katse ki. Ko da ba a kan gaskiya ki ke magana ba zai yi shiru ya saurare ki har sai kin gama bayaninki sannan ya fadi na shi ra'ayin.

3. Sun iya kwantar da hankali

Daga zarar sun fahimci rigima ki ke nema ko kina cikin damuwa suna saurin ganewa, saboda yanayin shirunsu kan sa su nakalci halayen mutane. Ko da ba ki yi magana ba zai fahimci cewa kina cikin tashin hankali ko damuwa, kuma ya san ta hanyar da zai bi wajen kwantar ma ki da hankali ta cikin ruwan sanyi ba tare da kin dagula ma shi lissafi ba. Ke ma kafin ki sani kin nemi damuwarki kin rasa. Suna da baiwa ta wannan fannin sosai.

4. Suna da saurin fahimtar yanayin mutane 

Komin surutunki akwai lokacin da zai zo ki ji ko motsi ma ba ki son yi. Ba wai dan kina cikin damuwa ba ko wani abu, hakanan za ki ta shi da canzawar yanayinki, ki ji ba ki son yi ma kowa magana.

Miskilin namiji zai yi saurin fahimtar har ya ba ki lokaci na kanki zuwa sanda za ki ji kin dawo hayyacinki, shi sam hakan ba matsala ba ce a wajen shi. Saboda ya san irin wannan yanayin da akan shiga, zai sa kanshi a ma'auninki. A lokacin ya ji irin abinda ki ke ji ta hakan zai saurara mi ki ya fahimce ki.

5. Ba su da saurin mita, gardama ko korafi

Akwai mazan da suna da mita da korafi, ko da kuskure ki ka yi ya kan dade kafin su manta, kullum sai sun yi ma ki mita akan abun. Koda kuwa kuskure aka samu ba halayyarki ba ce.

Amma su miskilan maza basu da wannan mita, ko gardama ce ta kaure su kan tsaya su natsu kafin su furtar da magana wadda idan suka yi, ta wadatar ba sai sun kara ba.

Daga lokacin da aka yi abu, suka yi magana shi kenan ya wuce a wajensu ba su sake maimaitar maganar bare su yi ma ki korafin kinyi kaza da kaza kwanaki ai.

6. Basu da nuna takama da alfahari

Ba kasafai za ki samu miskilin namiji da nuna isa ba, ya nuna shi ya isa a komi, usamman idan yana da kudi, ko kyau za ki samu wani ma ya zo yana alfahari da kudinshi, ya nuna cewa dan kudinshi ko kyan shi ki ke tare da shi. Irin wadannan kan so kansu fiye da yadda ki ke tsammani.

Amma miskilin namiji bai da wannan, bai ma da lokacin da zai tsaya batawa wajen yin haka.

7. Zama da miskilin kan koya ma ki yanda za ki so kanki ki yarda da kanki

Da yawan mata na fama da irin wannan matsalar ta rashin yadda da kai, wala Allah ta fannin sa sutura, iya kwalliya, kyawun sura, iya abinci da sauransu. Wata duk yadda ta kware a irin wadannan fannoni akwai lokuttan da za ta ji ai wance ta fita, sai a ga ta raina kanta tana ganin ai ba ta kai wance kyau ko iya kwalliya ba.

Miskilin namiji zai nuna ma ki cewa ai wancen ma kin fita, ko kuma ya nuna ma ki za ki iya yin fiye da ita. Zai karfafa ma ki gwuiwa sosai wajen tafiyar da rayuwarki saboda ba zai kushe ki ba.


8. Sun iya bada shawara

Saboda yanayin halayyarsu, mafi yawan lokuttan da ba magana su ke ba, su kan zauna su yi tunanin abubuwan da ke faruwa a rayuwa, idan da matsala tana za su nemo mafita. Su kan ba kansu wannan lokacin na tunani da samun warwara matsaloli.

A duk lokacin da ki ke neman shawara za su ba ki sahihiyar shawara ne, wadda za ta amfane ki ba kuma za ki yi dana sanin bin ta ba, saboda su din suna da kaifin basira da zurfaffan tunani.

9. Mutum ne shi mai gaskiya da amana

Abu ne mai matukar wahala ki samu miskilin namiji da rashin gaskiya ko rashin amana. Duk sirrinki a rufe suke a wajen shi saboda magana ma wahala take ba shi bare har ya zauna ya bada. Sannan baida yawaitar abokai da zai zauna ya fadi sirrinki a wajensu. Lokuttan shi na aiki ne, tunani ko karance-karance da rubuce-rubuce.

10. Mutum ne da idan yana son abu to yana son shi

Babu wani abu da zai canza hakan. Ya ganki da kwalliya ko ba kwalliya, zai so ki ne a yanda ki ke. Rashin kwalliyar ko kwalliyar ba zai taba canza yanda ya ke sonki ba.

11. Zama da shi kansa ki koyi wasu halaye na shi sannan ki kara sanin wasu abubuwan

A zama na farko abu ne mai matukar wahala ki fahimci waye shi, sannan baya daga cikin irin samarin da kan zo su yi bayyana ma ki kansu, wanda da wuya ki fahimci abu uku cikin bayanin da suke ma ki.

Miskilin mutum lokaci ne zai fada ma ki waye shi. A farko zai gundire ki, za ki yi ta korafin halayyarsa, amma da tafiya ta mika za ki fahimci cewa ya fi dadin zama.

Ke din da kanki za ki juya zuwa yanda ki ke so, ya danganta da ke din wacece. Dole ki nakalci abubuwan da ya ke so, dan ya zama akan su za ku tattauna. Ta nan za ki ji bakinshi fiye da yanda ki ke tsammani. Saboda kin tabo abinda ya ke so, musamman ma idan mutum ne shi mai son yawan karance-karance.


Posted by Ayeesh Chuchu 


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top