Wani matashi mai matsakaici shekaru da ba a kai ga gane ko waye ba ya gamu da ajalinsa a daidai lokacin da yake lalata da budurwarsa a garin Onitsha a jihar Anambra.

Majiyarmu ta shaida cewa, matashin ya yi ta ihu rike da kirjinsa yana cewa, ” kirjijna-kirjina” kimanin minti 30 bayan ya shiga dakin da ya kama a otel din.

Da yake tabbatar da lamarin mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda a jihar Anambra, SP Haruna Muhammad ya shaida cewa a ranar Alhamis da misalin karfe 7:45 na yamma manajan otel din Jubilee da ke Onitsha ya sanar da jami’an ‘yan sandan cewa, wani mutu bayan ya kama daki a otel din inda ya shiga da budurwarsa.

Bayan kimanin minti 30 sun juyo kururwarsa yana neman dauki yana “kirjina- kirjina” daga nan aka garzaya da shi asibiti, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa

Ya ce, babu alamun buguwa ko sara a gawar mamacin, “An kai gawarsa dakin ajiyar gawa na asibitin Boromeo domin bincike, yayin da hukumarmu ke ci gaba da bincikar lamarin,” in ji shi.

Post a Comment

 
Top