Mafi yawancin yan matan wannan zamanin zakaga suna soyayya da saurayi sunyi Amanna dashi har takai an sa ranar Aurensu

To Amma a gyefe guda kuma tana da wasu samarin da take kulawa bayan an samata Rana da wancan Na farkon

Sai kaga tana kulawa da samarin da suke zuwa zance gurinta fiye da yadda take kulawa da wanda Aka samata rana dashi,

Kuma mafi yawancinsu sunfi damuwa da saurayin da ba Aurensu ze yiba kome yasa haka?

Kuma mafi yawancin lokuta idan ka kirata a waya📲 zakaji tana waya da wani saurayin sa6anin kai da Aka samaku rana da ita,

Kuma wani Abun ban haushin sai ka tura mata kati domin ta kiraka dashi sai ta kira saurayinta, ko falashin bazatayima dashi ba har sai ya kare,

Da kace me yasa baki kirani ba sai tacema ai wata kawarta ta kira da katin sabo da tsabagen qarya,

Da ka kara tambayeta da dawa take waya sai tacema dan uwanta ne Haka zatai ta yaudararka soki-burutsun kalamanta,

A haka wasu samarin ransu yake 6aci suyi zuciya suje suce A basu kayansu da suka kawo sun fasa yin Auren su kuma yan matan sai su fara da nasani daga wannan lokacin,

Iyaye su rasa yaya Akayi wannan yaro yazo yace A bashi kayansa,
Ashe basu sani ba laifin yarsu ne,

Kuma Abunda zai kara baka mamaki shine wannan wanda take so din ba Aurenta zaiyi ba,
Kawai hangene irin nasu na mata 

Allah kaganar da yan matan wannan zamani su rika gane me sunsu da gaskiya,


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top