Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Masu Shirya Fina-Finan Hausa (MOPPAN) Kabiru Maikaba ya ce suna shirin fara hana masu shirya fina-finai yin fim din soyayyya don saboda su mayar da hankali kan wasu batutuwa na daban.
Maikaba ya shaida wa BBC cewa fina-finan soyayya ne kaso 80 cikin 100 na fina-finan Hausa.



"Me ya sa fina-finan soyayya kawai za mu rika yi bayan kuma akwai wasu bangarori da muke so a rika tabawa. Arewacin Najeriya yana da tarihi, me ya sa ba za mu yi wasa game da hakan ba," in ji shi.
Ya ci gaba da cewa: "Mun ce nan ba da jimawa ba, bayan babban zaben da za mu yi nan gaba kadan duk wani sabon fim da za a yi za mu bukaci sanin jigon labarinsa.

"Idan kuma muka ga na soyayya ne, to za mu dakatar da shi kuma za mu ci gaba da daukar wannan mataki har tsawon wani lokaci."
Ya ce bayan sun gamsu da yadda aka tabo wasu sassan rayuwa, za su ci gaba da yin fina-finan soyayyar.

Sai dai wasu masu shirya fina-finai sun fara tofa albarkin bakinsu kan wannan batu.
Ali Ali wani mai koyar da rawa ne a fina-finan Hausa ya ce hana su yin fina-finan soyayya kamar kashe harkar fina-finan Hausa ne.
"Na amince cewa ya dace masu shirya fina-finai su rika tabo wasu batutuwa bayan soyayya, amma ka ce kada a yi fim din soyayya hakan ba mai yiwuwa ba ne," in ji Ali Ali.

Daga nan ya ce ba ya ganin matakin zai shafe shi domin ya yi amannar cewa matakin ba zai yiwu ba.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top