Fitaccen mawakin Hausa kuma wanda yake fitowa a fina-finai Ado Gwanja ya ce tsabar yadda ya iya kwaikwayon 'yan daudu ne ya sa ake sa shi a fim din da ya danganci haka.
A wata hira ta musamman da ya yi da BBC Hausa, Gwanja ya ce duk wanda ya san shi ya san ba shi da wata alaka da 'yan daudu, "aiki ne za mu yi na fim da ya shafi daudun aka kira 'yan daudun sun fi su 50 amma suka kasa yi," in ji shi.
"To sai aka ce bari a gwada dan masana'antar Kannywood din, da aka gwada sai aka ga na ma fi su iya kwaikwayon abin sosai, shi kenan tun daga lokacin sai kuma ake yawan sa ni."

Gwanja, wanda wakokinsa suka shahara a kasar Hausa, haifaffen garin Kano ne, ya ce bai san me ya fi so ba tsakanin waka da yin fim, "kawai dai na san duka biyun ina son yin su sosai."

'Kokarin kwaikwayon Turawa ya sa ake yawan sukar 'yan Kannywood'
Cikinmu ya duri ruwa don tsoron rushewar Kannywood - Falalu Dorayi
Hadiza Gabon ta roki gafarar Allah kan 'kakkausan' martanin da ta yi a Twitter
Amma mawakin ya fara ne da yin waka, sai dai daga farko da ya ga ba ta karbu ba sai ya hada da fitowa a fina-finai.

Yawanci wakokin Gwanja sun fi farin jini a wajen mata saboda yadda yake wasa su, ya kuma ce yana hakan ne saboda "mata aka fi sani da son biki, to idan ba ka wasa su ba wa za ka wasa?"

Mawakin mai shekara 29 ya musanta cewa yana sa kalmomin batsa a wakokinsa kamar yadda ake zarginsa da yi, yana mai cewa da Hausa yake wakar ba wani yare ba, "kuma a sanina Bahaushe na da fahimta, kuma idan aka dauko wakokina a ka zube ba wacce ta shafi batsa."
Gwanja ya fara waka ne shekara 10 da suka wuce, kuma ya ce tsabar ra'ayinta ne ya sa ya fara.

Ya kara da cewa ba koya ya yi ba kuma ba gado ya yi ba, baiwa ce Allah ya ba shi. "Idan da gado zan yi ai sai dai na yi gadon dafa shayi, don mahaifina fitaccen mai sana'ar shayi ne a Kano," in ji Gwanja.

Hassada da kyashi


Kamar yadda yake a bayyane cewa mafi yawan jarumai ko mawaka na cin karo da matsaloli, sai dai Gwanja ya ce duk wanda ya samu kansa a matsala "to shi ya ga dama ya shige ta."
Kazalika mawakin ya ce shi a saninsa ba shi da wasu makiya ko abokan adawa a wannan harka, idan ma kuma akwai su to bai san da su ba. "Kazantar da ba ka gani ba kuma tsafta ce," in ji shi.

Wane ne Ado Gwanja?

Dan asalin unguwar Kofar Wambai ce ta Kano
Mahaifinsa shahararren mai shayi ne da ak fi sani da Gadagi Mai Shayi
Ya yi karatu har zuwa sakandare
Yana da mace daya da 'ya daya
Ya kan fito a fim kuma yana waka

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top