Share Dan Allah Al umma na Bukatar Sanin Wannan Bayani.

 Cutar lassa ta samo asaline daga beraye da gafiyoyi ko jaba. Wanda ahalin yanzu ta fara yaduwa acikin al'umma. Kuma har yanzu ba'a samar da wani ingantaccen maganin da zai iya yakar cutar 💯 alikitance ba. Amma amusulunce kamar yanda muka sani Allah bai saukar da wata cuta ba sai da ya fara saukar da maganin ta. Don haka yasa mukayi bincike na musamman akan wannan cutar tare da samar da maganin ta da yardar Allah.

ALAMOMIN KAMUWA DA CUTAR LASSA

1. Zazzabi
2. Amai
3. Gudawa
4. Fitar jina ta baki
5. Fitar jina ta hanci Da sauransu

HANYOYIN KARIYA DAGA KAMUWA DA CUTAR LASSA

 1. Kiyaye cudanya da m dauke da kwayar cutar.



2. Toshe hujunan beraye acikin gida ko daki.

3. Wanke kwanukan da suka kwana da sabulu kafin cin abinci.

4. Kula da matar da ta haihu, don jaririn zai iya daukar kwayar cutar daga wajen mahaifiyar sa.

5. Killace wadanda suka kamu da kwayar cutar
 awaje na musamman.

6. Zubar da duk wanni abinci ko gari ko wake ko danyar shinkafa da sauransu, wanda bera yaci ko yayi kashi ko fitsari akai tare da wanke kwanon da sabulu.

 YANDA ZA'A HADA MAGANIN LASSA

 Asamu garin Habbatus-sauda da saiwar tafashiya da ganyen runhu da ganyen rai-dore da ganyen katsari da citta da kusdul-hindi, ahadasu waje daya adaka atankade.

YANDA ZA'A BAWA MARAR LAFIYA MAGANIN

 Kafin a isa inda marar lafiya yake atabbatar, an sanya wadannan abubuwan kamar haka:-

 1-Safar hannu ta roda 2-Rufe baki 3 safar kafa 4-Gilashi(tabarau). 5.Hula ta musamman. 6Rufe ilahirin jiki da riga ta musamman.

AWUN SHAN MAGANIN

BABBA:- yasha cokali daya acikin ruwan dumi sau uku arana zuwa kimanin sati uku.
YARO:- Yasha rabin cokali acikin ruwan dumi sau biyu arana zuwa kimanin sati biyu.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top