An yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya, bisa samun ta da kotun ta yi da laifin kashe mijin ta, Bilyaminu Bello.

Babbar Kotun Abuja, FCT ce ta yanke mata hukuncin kisa, ba Babbar Kotun Tarayya ba, kamar yadda wasu suke ta watsawa.

Mai gabatar da kara ne tun a ranar da aka fara gurfanar da Maryam ya nemi Mai Shari’a ya yanke mata hukuncin kisa, kamar yadda doka ta tanadar wa wanda ya aikata irin laifin da ta aikata.
Laifin Maryam Sanda

Ta kashe mijin ta Bilyaminu da wukar yankan kayan miya (kitchen knife), cikin watan Nuwamba, 2017.

Mai Shari’a Yusuf Halilu ya ce Maryam ta cac-caka wa mijin ta wukar da niyyar kashe shi ne, ba kare kan ta ba.
Me Zai Biyo Baya?

Maryam za ta iya daukaka kara cikin kwanaki 90 bayan yanke mata hukuncin kisa da Mai Shari’a Yusuf Halilu ya yi a ranar Litinin.

Daga ranar da ta daukaka kara, tilas za a jingine hukuncin kisan, har sai kotu ta gaba ta yanke hukunci kenan.

Za a iya jaddada hukuncin da kotun farko ta yanke a kan ta. Idan kuma ta samu kwararun lauyoyi, kotun gaba za ta iya yi mata sassaucin daurin rai-da-rai, ko kuma na wasu shekaru masu yawa ko kuma wadanda ba za ta tsufa a gidan kurkuku ba.

Matsawar kotunan gaba suka jaddada hukuncin kisan, to babu makawa sai kisan ya tabbata.

Shugaban Kasa ne kadai zai iya yi mata afuwa, idan har yin hakan ya kama.

Yanke hukuncin kisa a Najeriya kamar ‘hangen Dala ne, amma ba shiga birnin Kano’ ba. Domin za ta iya yin sama da shekaru 10 a tsare, ba tare da an koma ta kan ta ba.

A jiha ba a zartas da hukuncin kisa a kan wanda kotu ta yanke wa, har sai Gwamnan Jiha ya sa hannu.

A kan kwashe shekaru da dama ba a samu wani gwamna ya sa hannu kan aiwatar da kisa a kan wani ko wasu da kotu ta yanke wa hukunci ba.

Tunda a Abuja aka yanke wa Maryam hukuncin kisa, Shugaban Kasa ne kawai zai iya yi mata afuwa. Saboda Abuja babu gwamna. Shi kuma Ministan Abuja doka ba ta ba shi ikon yi wa mai haddin kisa afuwa ba.

Wace Ce Maryam Sanda?

Maryam Sanda ba talaka ba ce, mahaifiyar ta tsohuwar Darakta ce a Abuja, a Aso Savings and Loans.

Mahaifin Maryam Sanda Fa
PREMIUM TIMES HAUSA na da tabbaci da hujjar cewa tun daga ranar da aka fara gurfanar da Maryam sanda a kotu, har ranar da aka yanke mata hukuncin kisa, mahaifin ta Sanda bai taba fashin zuwa kotun ba.

Don haka a gaban sa aka yanke wa ’yar ta sa hukuncin kisa. Ya na ji, ya na gani, ya na kuma saurare.

Abubuwan Da Suka Faru Bayan Maryam Ta Kashe Bilyaminu

23 Ga Nuwamba, 2017: Jami’an ’Yan Sanda sun gurfanar da Maryam a Babbar Kotun FCT, Abuja a ranar 23 Ga Nuwamba, 2017 –suka zarge ta da kash mijin ta, Bilyaminu Sanda.

24 Ga Nuwamba, 2917: Mai Shari’a Yusuf Halilu ya tura Maryam Kurkuku, bayan da ya hana lauyan ta beli.

Ranar 7 Ga Disamba, 2017: Kotu ta sake kin amincewa ta bayar da belin Maryam, ta sake tura ta ci gaba da zama a kurkuku.

Ranar 14 Ga Disamba, 2017: Kotu ta dai ki bayar da belin Zainab, amma ta bada belin wasu mutane uku da aka gurfanar da su tare, ciki kuwa har da mahaifiyar ta.

Ranar 7 Fabrairu, 2018: Wannan rana ma lauyoyin ta sun nemi beli, amma Mai Shari’a ya hana.

Ranar 7 Ga Maris, 2018: Mai Shari’a ya bada belin Maryam a bisa dalili na rashin lafiyar da kotu ta gamsu cewa Maryam din ke fama.

Ranar 19 Ga Maris, 2018: Mai gabatar da shaida ya fice daga kotun bayan ya isa, aka neme shi aka rasa.

Ranar 19 Ga Afrilu, 2018: Wani mai gabatar da shaida ya bayyana wa kotu yadda Maryam ta yi kokarin kisa ba sau daya, ba sau biyu ba akan mijin ta, a lokuta da dama.

Ranar 15 Ga Mayu, 2018: An samu tsaiko, shari’ar Maryam ta tsaya cak.

Ranar 3 Ga Oktoba, 2018: Lauyan da ke kare Maryam Sanda ya janye daga kare ta da ya ke yi a kotu.

Zargin Ganin Hotunan Tsiraici
Ranar 23 Ga Janairu, 2019: Maryam ta shaida wa kotu cewa hotunan tsiraicin wata mace da ta gani a cikin wayar mijin ta Bilyaminu, su ne suka yi sanadiyyar fada a tsakanin su, har ya gamu da ajalin sa.

Ranar 27 Ga Fabrairu, 2019: Kotu ta aza ranar da bangaren masu gabatar da kara da bangaren Maryam da ke kare kan ta, za su kammala bayanan su na karshe a kotu.

Ranar 26 Ga Maris, 2019: Kotu ta aza ranar da za ta yanke hukuncin da lauyan Maryam ya gabatar wa kotu cewa Maryam ba ta da laifi.

Ranar 4 Ga Afrilu, 2019: Kotu ta bayyana wa Maryam cewa tabbas akwai tuhumar da za ta amsa. Ta yi shirin kare kan ta kawai.

Ranar 8 Ga Oktoba, 2019: Kotu ta ce Maryam ta fara kare kan ta daga ranar 16 Ga Oktoba.

Ranar 2 Ga Disamba: Kotu ta bayyana cewa za ta yanke hukunci a kan shari’ar, a ranar 27 Ga Janairu, 2020.

Ranar 27 Ga Janairu, 2020: Kotu ta yanke wa Maryam hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Yau saura kwanaki 89 wa’adin daukaka kara ya cika.

Post a Comment

 
Top