Fitaccen mai bada umarni a fim, Yaseen Auwal ya tattauna da majiyar ta Northflix wanda ya tabbatar mana da cewar kasuwar Kannywood ba lalacewa ta yi ba face zamani da kuma sauyin da zamanin yazo dashi.
Yaseen Auwal, ya fadi hakan ne lokacin majiyar mu ta Northflix ta ke tattaunawa da shi dangane da sabon fim dinsa mai suna Mati a Zazzau dake shirin fitowa a gidajen haska fim.
Ga kuma yadda tattaunawar ta kasance da shi.
Akwai fim din ka Mati a Zazzau dake kan hanyar fitowa a sinima wanda tun kafin lokaci gari ya dauka kowa jiran fim din yake, me za ka iya cewa game da wannan fim?
“Alhamdulillahi shi Mati a Zazzau ai ba sabon fim ba ne, abun da ya sa na fadi hakan shi ne Mati a Zazzau ci gaba ne na wani gari to kuma mutane suna son su ga ya ya za ta kaya, shi ya sa za ki ga Jama’a duk gari ya dauka a na son a ga ya abuin yake. Sannan kuma suna sa ka ran za a kawo musu abu mai kyau wannan kawai shine dalili”. Inji  mai bada umarni.
Yawancin fina-finan ka bazan kira su na dogon zango ba kuma ba za a kira su na zamani ba. Kafin yin su kamar su Mati a Zazzau, me ya sa ka ke da ra’ayin bada umarnin irin wadannan fina-finan?
“Ai shi labari zuwa ya ke, inda fina-finan zamani bawai babu ba, saidai akwai abun da zai zo maka kai kuma ka na tunanin idan a kayi shi mutane za su karba su yaba, sannan kuma a na duba yanayin yadda rayuwa ta ke shi ma sai a yi shi wannan shine kawai”. Mai bada umarni Yaseen.
Ya ka ke ganin ci gaban Kannywood a halin yanzu, duba da irin yadda al’amura su ka sauya, ma’ana ka na ganin siyar da fina-finai a shafin internet na YouTube da sauran shafuka zai iya farfado da masana’antar Kannywood?
“Ai ba Kannywood ce a bar tausa yi ba, kasuwar fim ce ta duniya gaba daya, saboda idan ki ka duba da a na kawo fim a kaset na bidiyo a ka dawo na faifan CD a ka dawo na faifan DVD yanzu kuma a ka koma haskawa a sinima da kuma shafukan internet na YouTube duk da an dade a na nunawa a sinima amma ba kamar yanzu ba. Wanda duniyar yanzu da shi a ke amfani kuma muna sa ran mu ma nan bada jimawa ba zamu samu ci gaba sosai ta hanyar sinimar da kuma shafin YouTube din”. Yaseen
Matsayin ka na babban mai bada umarni, me ka ke ganin idan a ce za a kirkiro da shi yanzu zai iya farfado da masana’antar Kannywood, duba da yadda mutane ke korafin cewar Kannywood din ta yi kasa?
“Ai Kannywood ba ta yi kasa ba, yanayi ne ya canja kawai, idan mutum bai yarda da canjin da ta zo da shi ba, za ki gan shi ya koma baya a ka ce idan ko da kida ya canja sai rawa itama ta canja domin haka kannywood batayi kasa ba”. A Cewar mai bada umarni Yaseen Auwal


©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top